Auren Sha’awa Ake Yiwa ‘Yan Fim Shiyasa Aurenmu Baya Dadewa – Fati KK .
Ya zama kamar al’adar jaruman fim mata fitowa daga gidan mazajensu da zarar sunyi aure. Wannan yasa amihad.com ta kawo muku hira da wata jaruma wanda ita ma aurenta ya mutu..
A wata hira da aka yi da tsohuwar jaruma Fati KK ta bayyana cewa abinda maza ke bukata a jikin mace mai kyau irinta shine su aureta su gama jin dadinta su sake ta.
Ta ce yanzu ita tsoron sake yin aure take yi, saboda tana kallon maza duka halinsu daya ne.
Ta bayyana cewa ta fito daga wajen iyaye da suke da fahimta ga kuma ni’ima ta addinin Muslunci ita ce ta saka kullum take yiwa Allah godiya.
Majiyarmu ta samu wanna labari daga jaridar Blueprint, Fati KK tsohuwar ‘yar wasan fina-finan Hausa ce ta Kannywood wacce bata bukatar muyi dogon labari game da ko wacece saboda sunan da tayi lokacin da take masana’antar.
‘Yar asalin garin Kontagora ce dake jihar Neja. A lokacin da tauraruwar Fati ke haskawa kawai sai aka nemeta aka rasa abinda yasa masoyanta wasi-wasin inda ta shiga.
Comments
Post a Comment