maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen gwamnonin na ranar Asabar, 18 ga watan Maris, a jihohi 28 na ƙasar nan.
Farfesa Mahmood ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa da kwamitin tsaro kan zaɓe wanda akayo a ɗakin taro na INEC, a birnin tarayya Abuja, ranar Talata 14 ga watan Maris, 2023. Legit.ng ta rahoto
Shugaban hukumar zaɓen ya kuma bayyana cewa ba za ayi zaɓen gwamnoni ba a jihohi takwas.
Yayi bayanin cewa zaɓen gwamnonin jihohin da abin ya shafa ana yin sa a lokaci na daban ba lokacin gudanar da babban zaɓe ba.
Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da, Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Ondo, da jihar Osun.
“Za a gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohi 28 na ƙasar nan. Kamar yadda kuka sani zaɓen gwamnoni a jihohi takwa (Anambra, Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Ondo da Osun) ana yin su ne ba a daban ba lokacin babban zaɓe ba.”
“Sai dai, za a gudanar da zaɓe a mazaɓu 999 na jihohi a faɗin ƙasar nan.” A cewar shugaban INEC
Shehu Sani Ya Shawarci Shugaban Amurka JoeBiden Abinda Yakamata Ya Yiwa Tinubu
Comments
Post a Comment