maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan
Yanzu yanzu muke samun labarin cewa an yi musayar yawu tsakanin Reverend Joseph Hayab,Shugaban Kungiyar kiristoci na jihar Kaduna da kuma Ɗan takaran gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP Isa Ashiru Kudan.
Wannan zage-zagen ya biyo bayan wata takarda na sirri da Ƙungiyar kiristocin ta aike ma duk wani kirisita akan wanda zasu zaba a zaben gwamnan jihar Kaduna.
Sai da kuma takardan ta samu bullowa a kafafen yada zumunta na zamani.
Majiyar tamu tace Isa Ashiru bai ji dadin yadda takardan umurnin, wanda ke cike da yarjejeniyar da kiristocin suka yi da Isa Ashiru na irin muƙamai da ayyukan da zai ba kiristocin jihar Kaduna idan ya ci zaben gwamna.
Majiyar tace Ashiru ya kira Shugaban CAN ɗin ne, in da yake ce mai bai ji dadin ɓullar takardan ba.
Tun da sun yi akan cewa Ƙungiyar CAN ɗin tayi wa’azi ne a coci ranar lahadi a kan a zabe shi maimakon Jonathan Asake wanda yawancin kiristocin suka shirya zabe.
Shi kuma Shugaban CAN ɗin yace ma Ashiru ai ranar Litinin suka yi zaman su. Kuma idan akace za a bari sai Lahadi to lokacin an gama zabe. Don haka ba su da zabi illa su rubuta ta kafar sada zumunta na zamani. Kuma sun bada umurni ayi hankali wurin yaɗawa. Kar musulmai su gani.
Shine Isa Ashiru yace to ai abubuwan da CAN ta zaiyana a cikin umarnin, sun kara Zaburar da Musulmai ne.
Ya kawo aikin Naira Billion 3 ga Jami’ar KASU, Ashiru yace yunkurin dawo da reshen Jami’ar Jihar Kaduna da Makarfi ya kai Kafanchan. Yakowa kuma yaje yayi musu gine-ginen da ko Kaduna bai yi ba, Ya isa yasa duk wani musulmin jihar Kaduna ya zabi Uba Sani.
Tun da dama suna jin haushin kai kwasa-kwasai masu muhimmanci garin Kafanchan.
Ya kuma bude ma shugaban CAN din wuta akan cewa don me zasu fadi cewa Gwamna, deputy Gwamna, SSG, Chief of staff, Head of service,kashi tamanin na komishinoni,da manyan permanent secretaries duk musulmai ne. Wanda ba a taba samun haka ba sai wannan karan?
Daga karshe Ashiru ya nace lallai Kungiyar CAN sai ta fitar da sanarwa na biyu domin nesan ta kan ta ga waccan takardan. Kuma in zata yi, tayi kan wata takarda daban.
Comments
Post a Comment