maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
ME YA YI ZAFI? Yadda Wasu Daliban Jami'a Suka Yi Wa Wani Lakcara Dukan Tsiya A Jihar Yobe
...Kira na gaggawa ga ƙungiyoyin ɗalibai a Nijeriya
Ɗazu da safe Physicist Aminious Amin ya yi mentioning ɗina a wani shafi, inda aka wallafa faifan bidiyon yadda waau ƴan jagaliya suka samu Dr. Muhammad Saminu Dagari suka rufe shi da duka. Wasu da tsumagiya wasu da hannu. Don ƙarfin hali ma har da masu ɗauka da waya.
Dr. MUHAMMAD SAMINU DAGARI ba wai kawai malamin jami'a ba ne, a fagen kimiyyar CHEMISTRY irin sa ɗaiɗaiku ne da Allah (S.W.T) Ya azurta Nijeriya ta Arewa da ƙyanƙyasa. Malami ne ban mamaki, da Allah (S.W.T) Ya yiwa wata irin keɓantacciyar baiwa a fagen CHEMISTRY. Idan ana maganar Analytical Chemistry fannin da yake da ƙwarewa kenan (specialization), a nan kam an sallama masa ainun. Tsarekunsa da malamansa a department of Chemistry na BUK sun sallama masa sun ba shi kambi na sarauta a fagen Physical Chemistry.
Yana da rubuce-rubuce na nunawa a biki a fannonin Physical Chemistry, Inorganic Chemistry da Organic Chemistry. Dagari sarki ne mai rawani biyu, wanda kowane malamin CHEMISTRY yake cin arziƙin guminsa. Musamman a courses na Level 100 & 200, littattafansa su ne mafi girman madogara da ɗalibai da malamai ke komawa a BUK da KUST WUDIL. Idan ɗalibi ya karanta littafin Dagari ya yi masa kyakkyawar fahimta, to ya gama da duk wani surƙullen murɗa exam questions da malamin jami'a zai yi masa!
Dagari ba malamin CHEMISTRY ne a BUK ko KUST ko FUGashua ba, malamin duniya da aka dogara da fatawoyinsa da hukunsa akan mas'aloli masu nauyi. Yana da maƙalu na bincike (Researches & Journals) masu nauyin gaske da ƙima a duniyar CHEMISTRY, ba ma a ƙauyen Najeriya ba, waɗanda ya gabatar a manyan tarurrukan masana (conferences) na duniya. In ka san me ake nufi da #Q1 (First Quartile) na Academic Researches, to ayyukan Dagari sun isa wannan matakin!
Irin wannan malamin shi ne wasu ƴan iskan gari suka saka a gaba suna duka, saboda rashin mutunci da sanin ƙimar malami da ILIMI!
KIRA NA GAGGAWA!
Musamman zuwa ga:
• ASSUU
• V.C FUGashua
• National Association of Nigerian Students (NANS)
• BUK Alumni
• KUST Wudil Alumni
• HOD Chemistry department BUK
• National Association of Chemistry Students
•Students Chemical Society of Nigeria (SCSN) BUK chapter & KUST chapter
• National Association of Yobe State Students
• Students Union Government (SUG) FUGashua
• National Association of Physical Science Students (NAPSS) BUK, KUST & FUGashua chapters
An ci mutuncin babban malamin CHEMISTRY na Najeriya! An tozarta shi a idon duniya! Lallai ku tashi ku tabbatar da ƙwato ƴancinsa da ɗaukar matakin doka akan marasa mutuncin da suka yi wannan ɗanyen aikin!
In sha Allah za mu bi matakai na doka, wajen isar da wannan saƙo zuwa ga duk wanda ke da haƙƙin shiga ciki.
#Justice4Dagari
#NANS #BUK #KUST
#CHEMISTRY #ASUU
Comments
Post a Comment