maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Wani matashi ɗan Najeriya ya ankarar da mutane kan sabuwar hanyar da ƴan Yahoo suke amfani da ita suna kwashewa mutane kuɗaɗe Ta hanyar yin amfani da wayar sa, ya nunawa mutane yadda za su iya yin asarar kuɗaɗen su a asusun jihar su ba tare da sun bayyana lambobin katin ATM, lambobin sirri ko OTP ba Mutane da dama a soshiyal midiya sun yaba kan wannan muhimmin bayanin da yayi inda wasu daga ciki suka tabbatar da sun taɓa samun irin waɗannan saƙon nin.
Wani ɗan Najeriya mai suna Injiniya Victor, ya tona asirin wata sabuwar hanya da ƴan Yahoo suke amfani da ita wajen kwashewa mutane ƴan matsabban su. Ya bayyana cewa da wannan sabuwar hanyar, ƴan Yahoo suna kwashe kuɗi daga asusun mutane ba tare da katin ATM, lambobin sirri ko OTP ba.
Da yake nuna yadda suke yi, ya bayyana cewa abinda ƴan damfarar ke yi shine za su tura saƙonni barkatai ga wayoyin mutane. Victor yace suna samun lambobin wayar mutane ne ta wata manhaja ta musamman sannan mutane za su rasa kuɗin su da zarar sun bi umurnin da aka basu ko kuma suka danna kan saƙonnin da aka turo musu
Injiniya Victor ya bayyana cewa bankuna basu iya yin komai akai saboda a bayyane ake yi. Ya shawarci mutane da suka goge waɗannan saƙonnin da zarar an turo musu su a waya. Bidiyon na sa wanda Apostle Talker ya sanya a TikTok, ya ɗauki hankula sosai, inda mutane suka yi ta magana a kan sa.
Comments
Post a Comment