maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Tsoho Dan Kimanin Shekaru 75 Ya Dirkawa Yarinya Yar Shekaru 13 Ciki a Jahar Anambra
Tsoho Dan Kimanin Shekaru 75 Ya Dirkawa Yarinya Yar Shekaru 13 Ciki a Jahar Anambra
Wani Tsoho Kenan dan Kimanin Shekaru 75 daya dirkawa yarinya yar Shekara 13 ciki a jahar Anambra wanda ya bayyana cewa wasa ne Baiyi niyyar yin Hakan ba.
Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Anambra ta kuɓutar da wata yarinya ‘yar shekara 13 da ta haihu bayan da aka yi zargin mai kula da ita, Mista Sunday Muoghalu ya yi mata ciki.
A karshen makon daya gabata ne labarin haihuwar jaririn ya bazu a shafukan sada zumunta, inda ya nuna mahaifiyar matashiyar tare da jaririnta a wani asibiti da ke Adazi-Nnukwu a ƙaramar hukumar Anaocha ta jihar. Lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta neme ta bayan da wata ƙungiyar ma’aikatar mata tayi yunƙurin kuɓutar da ita.
Kakakin ma’aikatar, Chidimma Ikeanyionwu, a ranar Litinin, ya ce an kama Muoghalu a ranar Lahadi kuma aka miƙa shi ga hukumar ‘yan sanda. Mahaifiyar matashiyar ta ce ta fito daga jihar Akwa Ibom, yayin da iyayenta suka zauna a Agulu, jihar Anambra.
Wannan dai a yanzu zamanin da muke ciki ba wani abin mamaki bane domin anayi abubuwan da sukafi wannan ma sai dai ace Allah yakiyaye kawai. Mun gode da Ziyartar wannan Shafi namu wanda yake kawo maku labarai da dumi duminsu Mungode.
Comments
Post a Comment