maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
An Yankewa Matasa Uku Hukuncin Kisa ta Hanayar rataya bayan Fade da Kashe Wata Daliba da Sukayi a Jahar Kwara.
Wata babbar kotun jihar Kwara ta yanke wa wasu mutasa uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun su da laifin yiwa wata daliba mai suna Olajide Blessing Omowumi Yar Kimanin shekara 24 fyade tare da kashe ta.
An yanke masu wannan laifin ne a ranar Talata, 13 ga watan Disamba, bayan shafe shekara daya da rabi a shari’a. Idan dai za’a iya tunawa, an tsinci gawar dalibar ne a gidan Yar uwarta a ranar 2 ga watan Yuni, 2021, inda aka samu raunuka a al’aurarta, kuma bakinta ya tokare da tufafi.
Wani binciken gawar da wani likitan dabbobi a asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin, Dokta Kayode Adeniyi, wanda yayi magana da kotun ya tabbatar da cewa an yi mata fyade tare da shake ta har lahira.
Sannan an kama mutane takwas da ake zargi da hannu a kisan ta da wanda suka hada da Abdulazeez Ismail, Ajala Oluwatimileyin, Oyeyemi Omogbolahan, Abdulkarim Shuaib Kareem Rasheed, Abdullateef Abdulrahman, Daud Adebayo da Akande Taiye Oladojawere.
Mun gode da Ziyartar wannan Shafi namu wanda yake kawo maku labarai da dumi duminsu
Comments
Post a Comment