maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Dukkan Abunda Aka Mana na Kashe-kashe Sai Mun Rama__Al Zakzaky ya yi Alƙawari
Dukkan Abunda Aka Mana na Kashe-kashe Sai Mun Rama__Al Zakzaky ya yi Alƙawari
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Malam Ibraheem Zakzaky da Kotu ta sake a shekarar da ta gabata ya sha Alwashin dukkan abunda aka masa a Zaria na kashe Almajiransa da abubuwan da suka faru lallai baza su haƙura ba zasu rama, ya kuma jinjina ma waɗanda aka kashe a lokacin.
Yace: “Yanzu dai mulki ya yi muku daidai, amma nan gaba wani jininku –jikanku ko jikan jika, sai ya tsine muku albarka kafin al’umma ta karbe shi. Kuma ba wanda zai taba alfahari da sunanku, idan shi jikanku ne sai ya nemi a sakaya masa hakan ya buya ko kuma ya fito sarari ya tsine muku albarka kafin al’umma ta karbe shi. Wannan ina fada muku kamar ya auku, ai ba zan kasance ina nan ba, amma ta yiwu maganar da na yi ya wanzu a ji, amma insha Allahu abin da zai faru kenan.”
Comments
Post a Comment