maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Kalli Bidiyon Wata Budurwa Data Kusan Mutuwa Sanadiyyar Shaye-Shaye Kalli Bidiyon Anan
Cigaba da bayani kan Illolin shaye shaye…
Ita dai wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a cikin al’umma, matasa samari, yanzu abin tashin hankalin shine harda yan mata a harkar shaye shaye, kuma tabbas wannan matsala tanada matukar illa ga masu yinta da al’umma gaba ɗaya.
Illar shaye shaye ga lafiya.
~ Tana haifar da lalacewar huhu wato “lungs” ga masu ta’ammali da kayan hayaki.
~Tana haifar da magani yadena yiwa mutum aiki a lokacin da ake bukatar hakan, saboda jikinsa, ya riga ya raina adadin yadda zaiwa magani.
~ Kuma yakan taɓa kwakwalwa, wasu har haukachewa sukeyi gaba ɗaya.
A ɓangaren mu’amala.
Dan shaye shaye yana zama kamar mahaukaci acikin al’umma, saboda haka zai zamo abin kyama, Kuma shaye shaye nasa mutum ya zama mai dogon hannu wato “ɓarawo” tun daga gida har ta kai ga jama’ar unguwa, kuma sukan tsargu da kansu Dan haka ake saurin samun matsala dasu, Sai uwa uba, rashin girman na gaba, saboda Shaye shaye nasa mutum yaji dai dai yake da kowa.
ILLAR SHAYE-SHAYE A RAYUWA.
Ya kamata matasan arewa su nisanci shaye-shayen miyagun kwayoyi domin yin rayuwa Mai inganci.
Daga. YGM.
Kiran Rundunar matasan Mani ta Gabas ga iyaye da su tashi tsaye wurin kula da tarbiyar ‘ya’yansu matasa maza da mata.
Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma musamman ma matasa maza harda mata, masu aure da wadanda basu da shi.
Shaye-shaye na nufin duk wani yanayi da mutum zai sa kanshi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarinshi ta yadda ba zai iya auna yakamata ko akasin haka ba.
Shaye-shaye na zuwa ne a duk lokacin da mutum ya afka cikin Shan kwayoyi, sabanin yadda lilkita ya kayyade a sha, Shan giya ko tabar wiwi da dai sauran nau’ikan sinadarai masu bugar da mutum ko su Kai ga maye, da aikata wasu abubuwa na rashin hankali.
Wasu daga cikindalilan dake angiza wasu shiga shaye-shayen sun hada da jahilci, matsalolin rayuwa, al’ada, hulda da abokan banza, aikin karfi da kuma samun kyayoyin cikin sauki.
Shaye-shaye na zubar da mutunci, janyo talauci da jahilci, ciwon huhu, ciwon hauka, ciwon hanta, ciwon kansa, ciwon suga da kuma ciwon sanyin Kashi, sannan yana kawo lalaci da rashin kuzari, yadda Mai shaye-shaye ba zai iya katabus ba, tare da lalacewar mazakunta da dai sauransu.
Duk da irin kokarinda Gwamnati da hukumomi a matakai daban-daban ke gudanarwa wajen hana shaye-shaye, safarar kwayoyi da sauran kayan maye. Har ila yau ya zama dole iyaye su tashi tsaye don kula da tarbiyar’ya’yansu.
Sannan ya zama dole iyaye, manyan unguwa da sauran duk masu fada aji, a unguwanni su rika kula da harkokin yaransu na yau da kullum,l. Su kuma kula da irin abokai ko kawayen da yaransu ke hulda da su.
Dole ne Gwamnati, sarakuna, da malaman addinai suma su tashi tsaye wurin tsawatarwa da fadakar da al’umma illar shaye-shaye ta mahangar addini da rayuwa.
Dole ne kuma al’umma su bada hadin Kai wurin taimakawa jami’an tsaro da jami’an yaki da hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi wurin gudanar da aikinsu
ILLAR SHAYE-SHAYE GA MUSULMI
🚬• Duk musulmi mai tsoron ALLAH wanda yake tsaron haɗuwarsa da ALLAH to zai nisanci shaye-shaye.
🚬• Duk wanda yakeso ya kwanta a ƙabarinsa cikin lafiya da nutsuwa to bazai rinƙa shan koda sigari bace.
🚬• Duk wanda yake shan sigari to ka sani kana busawa ne akan mala’ikun ALLAH masu rubuta ayyukanka, wanda duk inda kake suna tare dakai,
🚬• Shin kana tunanin ALLAH bazai maka hisabi da cutarwar da kake musu ba, na hayaƙinta da warinta da kake busa musu?
🚬• Babu wani mashayin sigari da zaiyi sallah a masallaci alhali yana warin sigari malamai sukace sallarsa ba karɓaɓɓiya bace,
🚬• Domin Manzon ALLAH {s.a.w} yayi hani da wanda yake bakinsa akwai warin koda albasa ce, to ya nisanci masallaci, balle kuma sigari wacce ita haramunce.
🚬• Duk wanda ya kunna sigari a gaban al’umma yana sha yana kuma busa hayaƙinta, to shanta agaban mutane rashin kunya ne, rashin kunya kuma rashin imani ne da tsaron ALLAH, da kuma kafurcewa dokar ALLAH.
🚬• Sannan busar da ita a sama, to kana nunawa ALLAH TA’ALAH cewa bai isa ba, kana nuna rashin kunyarka ga ALLAH ƙarara, kana busa hayaƙin abinda ya hanaka a cikin baiwarsa wato iska.
🚬• Duk wanda yajewa matarsa yana warin sigari ya nemi yayi kissing nata ko yayi kwanciyar aure da ita, alhali yana warin sigari WALLAHI sai ALLAH yayi maka hisabi kaida ita akan wannan warin da kake bugo mata, duk mai auren da yake aikata haka to yaji tsoron ALLAH.
🚬• Babu wani yaro ko babba, mala’ika ko aljani ko dabba da zakasha sigari agabansa, face sai sun bada shaida akan shan sigarinka agaban ALLAH.
🚬• Babu wata gaɓa acikin jikinka da zakai amfani da ita, wajen shan sigari ko wee-wee face sai sun bada shaida agaban ALLAH akan abinda ka aikata dasu.
🚬• Babu wani guri da zaka tsaya ko ka zauna ka-sha sigari face sai ya bada shaida a gaban ALLAH akan abinda ka aikata akansa.
Allah ka karemu daga fadawa dabi’ar shaye shaye 🙏
Husseini na Azländ
Comments
Post a Comment