maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…
Mu Ƴan Fim Muna Da Tarbiyya Muna Kuma Koyar Da Ita – Ƴar Fim Zakiyya
Zakiyya Ibrahim wacce tauraruwar ta haskaka sosai a baya a masana’antar Kannywood, ta yi kira ga jama’a da su daina kallon ƴan fim a matsayin lalatattun mutane. Ta bayyana hakan ne a wata hira da Mujallar fim tayi da ita.
Ta shawarci abokan sana’ar ta ƴan fim
Jarumar ta kuma janyo hankalin abokan sana’ar ta na masana’antar Kannywood da su kiyayi yin abinda zai janyo musu magana.
“Mu ƴan fim mu na da tarbiyya,” inji ta
Jarumar ta koma sana’ar waka
Jarumar wacce yanzu ta rikide ta koma mawakiya ta kuma bayyana cewa tana samun alheri sosai tunda ta koma yin waka.
Ku Karanta Wannan: Ali Nuhu Ya Maka Jaruma Hannatu Bashir A Gaban Kotu
Ya zuwa yanzu dai ta yi wakokin siyasa masu yawa, inda ta fi samun kudi, ban da na yabon Manzon Allah (SAW) da na soyayya wadanda su ma ta yi su da dama.
“Kamar yadda na daɗe ina yin fim a matsayi na na jaruma, kuma haka na daɗe ina ɗaukar nauyin shirya fim. To ita ma waƙar haka na daɗe da ita.” Inji ta
Ta ci gaba da cewa:
“Tun a 2008 na fara waƙa lokacin da aka buɗe ‘Hikima’.”
“A gaskiya tun daga shekarar 2019 na fi mayar da hankali na a kan waƙoƙin siyasa, saboda su ne za ka yi a biya ka, tunda yanzu babu kasuwar sidi, to a haka na yi wa ‘yan siyasa masu yawa waka da gwamnoni da ‘yan majalisu.
“Kuma gaskiya ina samun alheri sosai.”
“Sannan kuma na bude shafi na a YouTube ina saka wakokin da na ke yi. Don haka ina samun cigaba sosai.”
Comments
Post a Comment