maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…

Image
  maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in… Alhamdu lillah shugaban kasa bula Ahmad tunubu ya umarci jami an tsarun costom nanbada jumawaba suye gaggawar bude boda yakuma kara daciwa ayehakuri wuyar da akasha a baya Kuma bayan wannan yakara daciwa matsalar man fetir ma zatazo karshi in Allah yayarda gaskiya dai bude buda za a samu saukin rayuwa inhaka ta tabbata

Yadda ɗan sanda ya ‘ɗirka wa ƴar ƙanwarsa ciki’ a Jihar Nasarawa

 








 ɗan sanda ya ‘ɗirka wa ƴar ƙanwarsa ciki’ a Jihar Nasarawa


Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta damke wani jami’inta mai mukamin insifekta, kan zargin yi wa wata ‘yar kanwarsa, ‘yar shekara 15 fyade, da yi mata cikin shege a Jihar Nasarawa.


An kuma kama wasu mutum uku, ciki har da wani likita, dangane da wannan aika-aika.


Kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya, wato FIDA, wadda ta bankado labarin afkuwar wannan lamari, ta ce za ta ci gaba da bin diddiƙin batun, har sai ta tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi a al’amarin.

 

Bayanan da BBC ta tattaro daga harabar hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa, sun nuna cewa an damke jami’in ɗan sanda mai mukamin sufeto, wanda ke aiki a sashen tattara bayanan sirri a wannan runduna.


Reshen Jihar Nasarawa na kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya ce ta bankado labarin wannan aika-aika, kuma take ta bibiyar lamarin.

 

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra, wadda ita ce shugabar ƙungiyar FIDA reshen Nasarawa ta bayyana cewa tun da farko sun samu rahoto ne daga wata cibiya ta tabbatar da adalci da zaman lafiya inda suka yi masu bayani kan wannan lamari.

 

“Da muka samu wannan labarin sai muka je B division a nan garin Lafiya muka je muka tarar da ƴan sanda sa’annan aka kama insifekta ɗin da matarsa da ɗansa,” in ji Barista Rabi’atu.

 

“Sai muka kai yarinyar asibiti aka je aka yi gwaji aka tabbatar tana da ciki wata shida amma kuma an so a zubar da cikin, ɗan da ke cikinta ɗin ya mutu har kwana uku yana cikinta.


Ta bayyana cewa a rana ta uku ce suka kai ta asibiti inda har ta haifi ƴa mace wadda tuni ta mutu a ciki inda ta ce jaririyar har ta soma ruɓewa.

Barista Rabi’atu ta ce yarinyar ta tabbatar cewa ɗan sandan ne ya yi mata ciki inda ta ce yakan dawo gida da lemu ko wani abin sha, amma ashe yana zuba mata wani magani ne a ciki, wanda duk lokacin da ta farka daga bacci sai ta ga jikinta duk ya ɓaci da jini.


A cewarta, sai daga baya yarinyar ta ankara ta gano cewa kawunta ne ke kwana da ita.

 

Barista Rabi’atu Ibrahim Addra ta ce, kungiyarsu ta FIDA ta lashi takobin yin tsayuwar daka, wajen ganin an gurfanar da masu laifi a lamarin, a kuma hukunta su, domin hakan ya zama wani kakkausan gargadi ga wasu.

Comments

Popular posts from this blog

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Fusata Zata Cirewa Mijinta Azzakari Saboda Ze Kara... 😭 Shiga Kaga Cikakkiyar Bidiyon Yadda Sukq Fafata... Me Zaku'iya Cewa?

Yanda Tahir Fage Ke Shan Soyayya Da Sabuwar Matarsa

innalillahi yanzu yanzu hatsarin mota yaye sanadiyyar motowar jikokin shiehk dahiru usman bauchi…