maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in…

Image
  maganar gaskiya akan bude bodar da shugaba tunubu yaye ga cikakken bay an in… Alhamdu lillah shugaban kasa bula Ahmad tunubu ya umarci jami an tsarun costom nanbada jumawaba suye gaggawar bude boda yakuma kara daciwa ayehakuri wuyar da akasha a baya Kuma bayan wannan yakara daciwa matsalar man fetir ma zatazo karshi in Allah yayarda gaskiya dai bude buda za a samu saukin rayuwa inhaka ta tabbata

Gwamnatin Kano ta fara rushe wasu gine-gine da ta ce an yi ba bisa ƙa'ida ba

 






Gwamnatin Kano ta fara rushe wasu gine-gine da ta ce an yi ba bisa ƙa'ida ba




Gwamnatin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara rushe wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnatin jihar.


A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ne bayar da umarnin fara rushe gine-ginen waɗanda ya ce an yi su ba bisa ƙa'ida ba a wasu wurare mallakar gwamnatin jihar.


Da safiyar ranar Asabar ne aka fara rusa wasu gine-gine a filin sukuwa a birnin domin ƙwato filin gwamnati kamar yadda sanarwar ta bayyana.


Idan za a iya tunawa a alƙawuran yaƙin neman zaɓe da gwamnan ya yi, ya alƙawarta ƙwato filaye mallakar gwamnati da aka gina ba bisa ƙa'ida ba.


Gwamnan ya ce za a rusa wuraren da aka gina a filayen makarantu da masallatai da filayen wasanni, da maƙabartu da kasuwanni da asibitoci, domin tabbatar da bin tsarin ginin birnin, tare da ƙawata shi da kuma tsare lafiyar al'ummar jihar.


Sanarwar ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su yi haƙuri, kasancewar sabuwar gwamnatin jihar na son tabbatar da ci gaban jihar.


Dama dai a jawabin da sabon gwamnan jihar ya yi bayan shan ranstuwar kama aiki ranar Litinin, ya bayar da umarni ga jami'an tsaro a jihar da su ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da ya ce tsohuwar gwamnatin Ganduje ta sayar wa wasu mutane a jihar.


A ranar Juma'a ne gwamnan ya bayar da umarni ga masu gine-gine a filin da ke bayan sansanin alhazai ( Hajj Camp) a jihar da su gaggauta dakatar da ginin nasu, bayan wata ziyara da ya kai wajen.



Comments

Popular posts from this blog

Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Fusata Zata Cirewa Mijinta Azzakari Saboda Ze Kara... 😭 Shiga Kaga Cikakkiyar Bidiyon Yadda Sukq Fafata... Me Zaku'iya Cewa?

Yanda Tahir Fage Ke Shan Soyayya Da Sabuwar Matarsa

innalillahi yanzu yanzu hatsarin mota yaye sanadiyyar motowar jikokin shiehk dahiru usman bauchi…